Manyan Labarai A Yau
Matsalar fasaha ta Cloudflare ta haddasa durkushewar shafukan intanet da dama, ciki har da X, ChatGPT da su Letterboxd yayin da kamfanin ke ci gaba da bincike.
Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani ta yi wa Nasir El-Rufai martani kan zargin ba 'yan bindiga makudan kudade har Naira biliyan daya.
Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya yi tsokaci kan matsalar rashin tsaro. Ya yi bayani kan rawar sa masu bada bayanai ke takawa wajen kai hare-hare.
Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ta yi wa Sanata Garba Maidoki martani. Ta zarge shi shi da yada bayanan karya kan rashin tsaro.
Babbar kotun tarayya Abuja ta karyata labarin cewa an yi yunkurin kashe Justice James Omotosho bayan hukuncin da ya yanke wa Nnamdi Kanu, tana kira da a yi bincike.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun yi wa jami'an 'yan sanda kwanton bauna a jihar Bauchi. 'Yan bindigan sun hallaka wasu daga cikin jami'an 'yan sandan.
Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya bayyana cewa ya fara shirin ganin an saki jagoran kungiyar 'yan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu, bayan yanke masa hukunci.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya damu matukan kan matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya. Ya ce gwamnatinsa na daukar matakai.
Rahotanni sun nuna cewa an jibge jami'an tsaro a ciki da wajem gidan yarin Sakkwato bayan labari ya nuna an kai mada jagoran IPOB, Nnamdi Kanu jihar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari