Manyan Labarai A Yau
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin rasuwar sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Ya ce rasuwarsa babban rashi ce.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci rundunar 'yan sandan Najeriya ta janye jami'anta da ke gadin manya. Sai dai a baya an sha yin irin wadannan alkawuran.
Rahotanni sun bayyana cewa za a gudanar da jana'izar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi a ranar Juma'a, 28 ga Nuwamba, 2025.
Gwamna Malam Dikko Radda ya sanya hannu a kudin kasafin kudin jihar Katsina na farko da zai lakume kudin da suka haura Naira biliyan 800, za a gina gobe.
Rundunar 'yan sandan Washington DC da ke Amurka, ta tabbatar da cewa an harbi sojojin kasa biyu har sun aamu raunuka a kuaa da fadar White House.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris Kauran Gwandu ya bada shawara ga daliban da 'yan bindiga suka saki. Ya ce musu su dauki lamarin a wani kalubale na rayuwa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasa (NIA), Ayo Oke, a matsayin Jakada. Ya taba shiga badakalar kudi a baya.
Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan rashin tsaro. Ta bayyana cewa gwamnati ba ta gayawa 'yan Najeriya gaskiya.
Rahotanni daga kasar Guinea-Bissau sun tabbatar da cewa dakarun sojoji sun kifar da gwamnati, sun sanar da dakatar da shirin zzabe tare da rufe iyakokin kasar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari