Manyan Labarai A Yau
'Yan ta'addan kungiyar ISWAP da suka yi garkuwa da wasu 'yan mata a jihar Borno sun bukaci a ba su miliyoyi kafin su bar su, su shaki iskar 'yanci.
Shugaban cocin INRI Evangelical Spirirual, Primate Elijah Babatunde Ayodele, ya fito ya gayawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu gaskiya kan rashin tsaro.
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a babban birnin tarayya Abuja, ta dage shari'ar da ake yi tsakanin hukumar EFCC da tsohon gwamnan Benue, Gabriel Suswam.
Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomowhole, ya soki sauya shekar da Atiku Abubakar ya yi zuwa jam'iyyar ADC. Ya ce ba zai iya gyara Najeriya ba.
Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta musanta batun kai hari a makarantar Government Girls College. Sun bukaci jama'a su yi watsi da labarin kai harin.
'Yan majalisar wakilan Najeriya daga yankin Kudu maso Gabas sun bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi afuwa ga jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.
Gwamnatin Birtaniya ta ki aminta da bukatar Najeriya ta neman dawo da Sanata Ekweremad ya ci gaba da zaman gidan yari a Najeriya duk da sa bakin Shugaba Tinubu.
Fadar shugaban kasa ta bayyana nasarorin da aka samu bayan tattaunawa da jami'an gwamnatin Amurka. Ta ce Amurka za ta hada kai da Najeriya kan rashin tsaro.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bukaci dakarun sojoji su canja tsari kan yadda suke fuskantar matsalar rashin tsaro. Ya koka kan sace dalibai a jihar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari