Manyan Labarai A Yau
Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun yi artabu da wasu 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno. Sojojin sun kashe 'yan ta'adda masu yawa.
Tsohon ministan shari'a a karkashin gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, Abubakar Malami ya amsa gayyatar da hukumar EFCC ta yi masa don amsa tambayoyi.
Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta gayyaci tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2027, Dati Baba Ahmed kan zargin yin wasu kalaman tunzura jama'a.
'Yan bindigan da suka yi garkuwa da mataimakin shugaban karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina sun sake shi. Sun sake shi bayan an bada kudin fansa.
Hedkwatar tsaro ta fara gudanar da bincike kan sojojin da suka janye daga makarantar GGCSS Maga, kafin kawo harin 'yan bindiga. An fara gudanar da bincike.
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya nuna takaicinsa kan yadda matsalar rashin tsaro ke kara tabarbarewa. Ya bukaci gwamnati ta daina tattaunawa da yan bindiga.
Gwamnatin jihar Kano ta yi kira ga hukumomin tsaro su damke tsohon ahugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje kan shirinsa na kafa rundunar Hisbah.
A makon da ya gabata ne aka yanke wa shugaban IPOB, Nnamdi Kanu hukuncin daurin fai da rai, ya shiga jerin wadanda suka wakilci kansu a kotu babu lauya.
Tsohon ministan kwadago, Dr. Chris Ngige, ya bayyana cewa yana nan a raye bayan wasu yan bindiga sun farmake shi a kan wani titi a jihar Anambra.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari