Manyan Labarai A Yau
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani mummunan harin 'yan bindiga a jihar Zamfara. Sojojin sun kuma kwato makamai daga hannun tsagerun.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar ministoci 2 da wasu mutum 6 a hatsarin jirgin saman da ya auku a Ghana, ya roki Allah Ya masu rahama.
Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris watau Kauran Gwandu ya amince da raba yankin hakimin Maiyama gida biyu, ya sanar da sababbin hakiman da za su jagorance su.
Rahoton kwamitin bincike da aka kafa a Kano ya gano abubuwa da dama game da laifin da ake zargin tsohon kwamishinan sufuri, Ibrahim Ali Namadi da aikatawa.
Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Babatunde Ayodele, ya bayyana cewa jam'iyyar ADC za ta iya kifar da wasu gwamnonin Najeriya.
Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro a yankin Arewa maso Gabas, sun samu nasarar hallaka 'yan ta'addan Boko Haram yayin wani artabu.
Wani jigo a jam'iyyar APC daga Arewacin Najeriya, Alwan Hassan, ya bayyana cewa yankin Arewa ba zai zabi Peter Obi ba a 2027 saboda yana sana'ar shigo da giya.
Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattWa, Sanata Shehu Sani, ya kare Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matsalolin da suka addabi Arewa.
Wani dan majalisar wakilan Najeriya a jihar Zamfara ya kaddamar da aikin gyaran makabartu. Ya bayyana cewa hakan yana da muhimmmanci ko a addini.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari