Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana kudin da ya tarar a asusun jihar. Gwamna Fubara ya ce kafin dakatar da shi, ya bar makudan kudi har N300bn.
Tsohuwar uwargidan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta yi bayani kan mulkin mijinta na shekara takwas. Aisha Buhari ta bayyana kuskuren da ya yi.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ba da tabbacin cewa ba zai sauya sheka daga jam'iyyar PDP mai adawa zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ba.
Jam'iyyun siyasa daban-daban na da gwamnoni a jihohin Najeriya. Jam'iyyar APC na kan gaba da mafi yawan gwamnoni. PDP da sauran jam'iyyun adawa na take mata baya.
Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya kaddamar da majalisar masarautun Katsina domin karfafa hadin gwiwa tsakanin gwamnati da sarakuna kan tsaro.
Majalisar dattawan Najeriya ta nuna fushinta kan jita-jitar da aka rika yadawa ta rasuwar shugabanta. Ta bukaci a hukunta masu yada zuki ta mallen.
Wani sabon littafi da aka kaddamar kan marigayi Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da ya sa tsohon shugaban kasar bai goyi bayan takarar Yemi Osinbajo ba.
An yada wasu rahotanni masu nuna cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya yanke jiki ya fadi sakamakon rashin lafiyar da ya kama shi.
Tsohon Babban Alkalin Alkalai na Najeriya, Justice Ibrahim Tanko Muhammad, ya rasu a Saudiyya yana da shekaru 71, lamarin da ya jefa kasa cikin jimami.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari