Manyan Labarai A Yau
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kira hafsoshin tsaro zuwa fadarsa da ke Aso Rock Villa a Abuja. Sun shiga wata muhimmiyar ganawa ta sirri a tsakaninsu.
Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya yi tsokaci kan matsalolin da ake fuskanta. Ya ce matsalar rashin tsaro na bukatar hadin kai.
Tinubu ya yabawa marigayi Muhammadu Buhari a Abuja, yana bayyana shi a matsayin abin koyi na gaskiya, rikon amana da hidimar kasa a tarihin Najeriya.
Ana sa ran Najeriya za ta ayyana hutun Kirsimeti, Boxing Day da sabuwar shekara na Disamba 2025 da Janairu 2026, inda ake sa ran za a rufe wuraren aiki.
Tsohon Antoni Janar kuma Ministan shari'a, Abubakar Malami, ya bukaci shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), ya cire kansa a bincikensa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin rasuwar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Lawrence Ewhrudjakpo. Ya bayyana shi a matsayin jajirtaccen mutum.
Kotun Koli ta tabbatar da ikon shugaban kasa na ayana dokar ta-baci a jihohi, da kuma ikon dakatar da zababbun gwamnoni a shari'ar da gwamnoni PDP suka shigar.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa sabuwar runduna ta musamman wadda za ta rika kula da tashoshin motoci da sauran wuraren da jama'a ke taruwa.
Tsohon jakadan Najeriya a kasar China, Sheikh Uthman AbdulAzeez, ya riga mu gidan gaskiya, Gwamna AbdulRahman AbdulRazak na jihar Kwara ya yi ta'aziyya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari