Manyan Labarai A Yau
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya taba fuskantar yunkurin juyin mulli lokacin da yake kan mulkin farar hula. An cafke sojojin da ake zargin suna da hannu.
Majalisar tarayya ta gabatar da wasu kudirori gaban shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin neman amincewarsa da rattta musu hannu. Sai dai bai yi hakan ba.
Wasu 'yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari a jihar Zamfara inda suka yi awon gaba da mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Jam'iyyar hadakar yan adawa watau ADC ta dakatar da Dr. Usani Usani, mataimakin shugabanta na kasa mai kula da shiyar Kudu maso Kudu jan zargin cin amana.
Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta bayyana cewa yawan sauya shekar da jiga-jigan 'yan adawa suke yi zuwa APC, ba zai hana jam'iyyar faduwa ba a zaben 2027.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tababtar da tsare wani dan jarida bisa zargin bata sunan hadimin gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf. Ta ce ana yin bincike.
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta dakatar da shugabanta a jihar Edo. Jam'iyyar ta bayyana cewa an dakatar da shi bayan an same shi da wasu laifuffuka.
Jiragen yakin rundunar sojojin saman Najeriya sun yi ruwan wuta kan 'yan bindiga a jihar Neja. Farmakin ya jawo an hallaka 'yan bindiga masu yawan gaske.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya gamsu da irin goyon da jam'iyyar APC ke samu. Ya bayyana cewa za ta samu kuri'u masu yawa a zaben shekarar 2027.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari