Manyan Labarai A Yau
Gwamnonin jam'iyyar PDP da sauran masu ruwa da tsaki daga Arewa, sun amince da Saminu Turaki a matsayin dan takararsu domin zama shugaban jam'iyyar na kasa.
Babban hafsan tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa, ya bayyana cewa nan da wani lokaci kadan za a kawo karshen ayyukan 'yan bindiga da 'yan Lakurawa.
Gwamnatin Osun ta nada Davido shugaban asusun tallafawa wasanni, domin janyo jari da inganta harkar wasanni, yayin da ake gyaran filin wasa na Osogbo.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi artabu da 'yan bindiga a jihar Zamfara. Sojojin sun samu nasarar fatattakar 'yan bindigan wadanda suka zo daukar fansa.
Kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ta yi alhini da jimamin mutuwar mutane sama da 40 a hatsarin fashewar tankar mai da ya auku a jihar Neja jiya Talata.
Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya nuna cewa da wuya a iya samun shugaban da zai yi nasara idan Mai girma Bola Tinubu ya gaza a mulkin Najeriya.
Mahaifin marigayiya Somtochukwu Maduagwu, ’yar jaridar Arise TV, ya zargi cewa an kashe ’yarsa da gangan, yayin da ’yan sanda suka kama mutum 12 da ake zargi.
Kungiyar dattawan jam'iyyar PDP na Arewacin Najeriya, sun caccaki ministan babban birnin tarayya Abuja. Sun zarge shi da yunkurin ruguza jam'iyyar PDP.
An yi muhawara mai zafi a Majalisar Dattawan Najeriya kan kudirin dokar zubar da ciki a Najeriya, Sanata Akpabio da Natasha sun yi musayar yawu bayan rufe batun.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari