Manyan Labarai A Yau
Dan Majalisar Wakilan Tarayya, Hon. Garba Muhammed ya koka kan barazanar da ya ce ana masu da rayuwa, ya ce yan ta'addada da masu zanga-zanga sun yi barazana.
Majalisar dattawan Najetiya ta karbi sunayen sababbin hafsoshin tsaro daga wajen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Majalisar ta sanya lokacin tantance su.
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bukaci ministoci su rika gayawa shugabannin kasa gaskiya komai dacinta. Ya ce ya kamata su daina kwarzanta su.
Wasu masu safarar miyagun kwayoyi sun kai farmaki kan jami'an hukumar NDLEA da sojoji a jihar Edo. An kai farmakin ne domin hana su gudanar da aikinsu.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya bukaci majalisa ta kara karfafa tsarin dokokin zabe na kasar nan.
Atedo Peterside, shugaban gidauniyar Anap kuma wanda ya kama bankin StanbicIBTC ya ce mulkin Mahmud Yakubu a INEC abin kunya ne ga kasa kamar Najeriya.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a jihar Kano. 'Yan bindigan sun hallaka wani mutum tare da sace kayayyaki masu yawa yayin harin.
Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta yi watsi da barazanar kai ta kara gaban kotu da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi kan kasa sayen fom din takara.
'Yar takarar gwamnan jihar Anambra karkashin inuwar jam'iyyar AAC, Chioma Ifemudilike, ta yi alkawarin kyautata jin dadin ma'aikata ta hanyar kara musu albashi.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari