Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya yi garambawul a gwamnatinsa. Gwamnan ya sauya wa wasu daga cikin kwamishinoninsa ma'aikatun da za su jagoranta.
Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya bayyana tsare-tsaren da suka yi na birne mataimakinsa, Mr Lawrence Ewhrudjakpo, wanda ya rasu a watan Disamba, 2025.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi tsokaci kan sauya sheka zuwa jam'iyyar APC. Ya ce dole ne ya san matsayarsa kafin ya koma.
Dan wasan gaba na Najeriya, Victor Osimhen ya bayyana cewa tawagar Super Eagles ba ta jin dar-dar kan karawa da takwararta ta Morocco a gasar AFCON 2025.
Wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin jihar Rivers sun janye daga shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara. Sun bayyana dalilin da ya sanya suka yi hakan.
Fitaccen dan jarida a Najeriya kuma daya daga cikin wadanda suka kafa jaridar Newswatch, Yakubu Mohammed ya rasu bayan fama da doguwar jinya a jihar Legas.
Shugaban kwamitin shugaban kasa kan gyaran haraji, Taiwo Oeyedele ya bayyana halin da rayuwarsa ta shiga kan kokarinsa na ganin an gyara tsarin haraji.
Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta karfafa gwiwar tawagar 'yan wasan Super Eagles kan wasan da su yi da Morocco.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bukaci jama'a ka da su tsaya suna fada da miyagun masu aikata laifuffuka. Ta ce kare rai ya fi tsayawa yin fada.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari