Manyan Labarai A Yau
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bar Najeriya zuwa kasar waje. Shugaba Bola Tinubu ya yi tafiya ne zuwa kasar Turkiyya inda zai gudanar da wasu muhimman abubuwa.
An cire duka tutocin jam'iyyar NNPP tare da maye gurbinsu da na APC yayin da ake shirin karbar Gwamna Abba Kabir Yusuf a hukumance yau Litinin, 26 ga watan Janairu.
Jigo a jam'iyyar APC, Farfesa Haruna Yerima, ya yi magana kan batun sauya tikitin Tinubu/Shettima a zaben 2027. Ya bayyana babban kuskuren da APC za ta yi.
Shugaban hukumar kula da allunan tallace-tallace ta jihar Kano (KASA), Kabiru Dakata, ya kare Gwamna Abba Kabir Yusuf kan shirin da yake yi na komawa APC.
Jam'iyyar LP ta samu nasarorin da ba a yi zato ba a zaben 2023 sakamakon tasirin Peter Obi da goyin bayan matasa, sai dai ta gamu da tangarda bayan zaben 2023.
Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da cafke wata amarya bisa zargin kashe mijinta har lahira. Amaryar ta amsa cewa auren dole iyayenta suka yi mata.
Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta yi magana kan yiwuwar shigowar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa cikinta. Ta bayyana cewa tana maraba da shi da tawagarsa.
Wanda ya kafa jam'iyyar NNPP, Dakta Bonieface Aniebonam, ya bayyana cewa gwamnan Kano, Mai girma Abba Kabir Yusuf bai yi murabus daga jam'iyyar ba.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi magana kan makomar jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2027. Ya ce masu sukar jam'iyyar za su sha mamaki a zaben 2027.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari