Manyan Labarai A Yau
Wasu daga cikin gwamnoni 36 na Najeriya sun kasance tsofaffin sanatoci. Wadannan gwamnonin sai da suka fara zuwa majalisa kafin au dawo jagorancin jihohinsu.
Babban alkalin jihar Katsina ya yi tsokaci kan batun sakin wasu daga cikin 'yan bindigan da aka tsare. Ya bayyana cewa gwamnati ta nemi shawara ta fuskar shari'a.
Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya yi tsokaci kan zargin yin cushe a dokokin haraji. Sanata Ndume ya ce akwai bambanci a abin da Tinubu ya sa wa hannu.
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya yi magana kan jita-jitar cewa ya gana da Rabiu Musa Kwankwaso. Fayemi ya fadi alakar da ke tsakaninsu.
Shugabar hukumar NIDCOM, Abike Dabiri-Erewata ce jami'an gwamnatin kasar Turkiyya sun yi mamakin yadda tuntuben Tinubu ya dauki hankali a Najeriya.
Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin Gwamna Nasir Idris, ta bullo da shirin horas da 'yan banga don tunkarar matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.
Rahotanni sun bayyana cewa jirgin saman ya bata ne dab da zai sauka a yankim bodar Colombia da Venezuela, wanda yan tawaye ke da iko da shi, an fara bincike.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi barazanar farmakar kasar Iran kan shirinta na nukiliya. Ya ce dole ne ta gaggauta zama nan teburin tattaunawa.
Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi, ya soki harin da Amurka ta kawo a Najeriya. Ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya yi kuskure.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari