Manyan Labarai A Yau
Wasu masu ruwa da tsaki a APC ta jihar Enugu sun bayyana damuwarsu kan yadda wasu jagorori ke neman toshe lafar sauya shekar gwamna Peter Mbah zuwa APC.
An yada wata jita-jita mai cewa tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ya fice daga jam'iyyar. Shugaban APC a karamar hukumarsa ya yi bayani.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin kwanton bauna kan jami'an tsaro a jihar Benue. Ana fargabar cewa an hallaka sama da jami'ai guda 10.
Kasashen Birtaniya, Canada da Austalia sun bi sahun masu amince da kafa kasar Falasdinu. Ana sa ran wasu kasashe za su bi bayansu a taron majalisar dinkin duniya.
Kungiyar APC North Central Forum ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi kaffa-kaffa da wasu gwamnonin jam'iyyun adawa kan zargin muzgunawa 'yan APC.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya gargadi 'yan Najeriya kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. El-Rufai ya ce yana shirin mulkin kama karya.
Ba tare da lambar TIN ba, mai biyan haraji ba zai iya amfani da asusun banki, inshora, asusun fansho, ko asusun zuba jari ba, kuma, zai fuskanci hukunci daga 2026.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun tafka ta'asa yayin da su ka yi awon gaba da hadimin gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule. Sun sace shi ne a gidansa.
Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, ya nada sababbin sarakunan Yarbawa 20 a masarautar Ile-Ife, ya bukace su akan yin mulk da tawali’u, hikima da hidima ga jama’a.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari