Manyan Labarai A Yau
Fadar shugaban kasa ta bayyana nasarorin da aka samu bayan tattaunawa da jami'an gwamnatin Amurka. Ta ce Amurka za ta hada kai da Najeriya kan rashin tsaro.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bukaci dakarun sojoji su canja tsari kan yadda suke fuskantar matsalar rashin tsaro. Ya koka kan sace dalibai a jihar.
Iyalai sun tabbatar da raauwar tsohon hadimin gwamnan jihar Legas, Alhaji Lateef Jakande yana da shekaru 75 a duniya, za a sanar da lokacin jana'izarsa.
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa ba za ta kulle makarantu ba, saboda matsalar rashin tsaro. Ta bayyana cewa ta dauki matakan da suka dace.
Tsohon hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa 'yan kasar waje ba za su iya ceto Najeriya ba kan matsalar rashin tsaro.
Kasar Amurka ta yi magana kan satar dalibai da aka yi a jihohin Kebbi da Neja. Ta bukaci hukumomi su gaggauta ceto yara 'yan makaranta da aka sace.
Jagoran yan adawar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya yanki katin zama cikakken mamba a jam'iyyar hadaka watau ADC a mazabar Jada da ke jihar Adamawa.
Sanannen malamin addinin Musuluncin, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya bayyana cewa babu wata gwamnati da za ta iya kawo karshen matsalar rashin tsaro.
Matsalar fasaha ta Cloudflare ta haddasa durkushewar shafukan intanet da dama, ciki har da X, ChatGPT da su Letterboxd yayin da kamfanin ke ci gaba da bincike.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari