Manyan Labarai A Yau
Rahotanni daga kasar Guinea-Bissau sun tabbatar da cewa dakarun sojoji sun kifar da gwamnati, sun sanar da dakatar da shirin zzabe tare da rufe iyakokin kasar.
Sanatoci sun kai ruwa rana kan matsalar tsaron da ke kara ta'azzara a wasu sassan Najeriya, wasu sun bukaci a yi dokar hukuncin kisa kan masu garkuwa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada jakadu wadanda za su rika wakiltar Najeriya a kasashen waje. Hakan na zuwa ne bayan ya kwashe fiye da shekara biyu a mulki.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana cewa ko sisin kwabo gwamnati bata biya 'yan bindiga ba kafin su sako daliban da suka sace a jihar Kebbi.
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya koka kan matsalar rashin tsaro. Atiku ya ce 'yan bindiga na cin karensu babu babbaka.
Gwamna Ahmed Ododo ya bayyana irin halin da ya shiga lolacin da ya samu labarin rasuwar Sarkin Bassa Nge kuma tsohon gwamnan Bauchi na soji, Abu Ali.
Hukumar kwastam ta bullo sa tsarin gwada lafiyar jami'anta. Hukumar ta umarci a fara yin gwajin miyagun kwayoyi ga sababbin jami'ai da wadanda ke aiki a yanzu.
'Yan ta'addan kungiyar ISWAP da suka yi garkuwa da wasu 'yan mata a jihar Borno sun bukaci a ba su miliyoyi kafin su bar su, su shaki iskar 'yanci.
Shugaban cocin INRI Evangelical Spirirual, Primate Elijah Babatunde Ayodele, ya fito ya gayawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu gaskiya kan rashin tsaro.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari