Manyan Labarai A Yau
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya ki yarda ya bi jami'an tsaro saboda babu wata takardar gayyata da aka turo masa a hukumance.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gabatar da kasafin kudi don zaben shekarar 2027. INEC ta bayyana cewa hakan ya yi daidai da tanadin doka.
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima, ya yi tafiya zuwa kasar Ethiopia. Shettima zai wakilci Mai girma Bola Tinubu a wajen taron kungiyar AU.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi sababbin zarge-zarge kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ya ce za su yo kokarin murde zaben 2027.
Alkali Obiora Egwuatu ya janye daga shari’ar tsohon Minista Abubakar Malami kan zargin N212bn a Abuja. Ya bayyana hakan ne a zaman kotu na yau 12 ga Fabrairu, 2026.
Nasir El-Rufai zai dawo Nijeriya nan da sa'o'i 48 domin amsa kiran EFCC a ranar 16 ga Fabrairu, 2026. Ya musanta zargin tserewa zuwa waje don gujewa masu bincike.
Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri, ya goyi bayan Bola Tinubu a zaben 2027, yana jaddada amfanin manufofin gwamnatinsa ga talakan Najeriya.
Jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya ta yi martani kan shirin da Amurka ta fara na kakabawa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, takunkumi. Ta fito ta kare shi.
Ministan ayyuka, David Umahi, ya kare matakin da aka dauka na ba da kwangilar aikin titin Kaduna zuwa Abuja. Ya shirya yin murabus idan aka samu matsala.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari