Manyan Labarai A Yau
Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, Ali Ndume, ya yi hannunka mai sanda ga jam'iyyar APC. Ya ja kunnenta kan jam'iyyar adawa ta ADC.
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El Rufai ya yi ikirarin cewa ya saurari wayar Nuhu Ribadu, inda ya ji lokacin da yake ba da umarnin a kama shi a tsare.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi zarge-zarge kan jam'iyyar APC mai mulki. Ya ce tana shirin raunana ADC bayan ta ruguza PDP.
Wani jigo a APC, Cif Eze ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na fargabar zaben 2027 duk da mafi yawan gwamnoni na tare da shi a jam'iyyar APC.
Gwamnatin tarayya ta sake dauko batun janye 'yan sanda daga gadin manya. Gwamnatin ta bayyana inda ta tura 'yan sandan da ke gadin manyan mutane a kasar nan.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027. Ya ce ya kamata Arewa ta sake zabensa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai tarbi gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyyar APC. An shirya gagarumin bikin tarbar gwamnan zuwa APC.
Majalisar dokokin jihar Kaduna ta yi martani kan rahotannin da ke cewa 'yan ta'adda sun yi garkuwa da daya daga cikin mambobinta. Ta ce labarin kanzon kurege ne.
Hadimin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kafafen yada labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya yi magana kan batun tura sakamakon zabe ta yanar gizo.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari