Manyan Labarai A Yau
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Abuja, ta ba hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), umarni kan yi wa jam'iyyun siyasa rajista a Najeriya.
Babban jigo a jam'iyyar APC, Alhaji Sani Shinkafi, ya yi magana kan zaben shekarar 2027. Jigon na APC ha fito ya ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu shawara.
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta rage lokacin da ma'aikata za su rika tashi daga aiki. Ta saukaka musu saboda azumi.
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi bayani dalla-dalla bayan ya sanya hannu a dokar zabe. Ya ce za a ci gaba da yin zabe ta hanyar dangwala wa.
Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya bayyana cewa bai karbi ko sisin kwabo da sunan ladan sauya sheka daga PDP zuwa APC ba, ya ce bisa ra'ayin kansa.
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya aika da sakon neman yafiya a wajen 'yan Najeriya. Shugaba Tinubu ya bukaci a yafe masa idan ya aikata ba daidai ba.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris Kauran Gwandu, ya saukakawa ma'aikata saboda azumin watan Ramadan. Gwamna Nasir rage musu lokacin tashi daga aiki.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika sako ga al'ummar Musulmai da Kiristoci a Najeriya. Ya bukaci su yi amfani da lokutan ibada na azumin Ramada da Lent.
Rahotanni daga karamar hukumar Wase ta jihar Filato sun tabbatar da mutuwar mutane 37 sakamakon shakar iskar gas mai guba a ramin hakar ma'adanai.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari