Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya fasa kwai kan matsalar garkuwa da mutane da ake fama da ita. Ya nuna yatsa ga 'yan siyasa masu neman mulki.
Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe-korafen jama'a ta jihar Kano (PCACC), Muhuyi Magaji, ya bayyana dalilin da ya sa 'yan sanda suka kama shi.
Jam'iyyar YPP ta tatttara wa dan Majalisa, Hon. Uzokwe Peter kayansa ta kore shi daga jam'iyyar bayan ganin bidiyon shaidar irin cin amanar da yake mata.
Gwamnatin jihar Sokoto ta yi martani kan zargin cewa Gwamna Ahmed Aliyu ya raka takwaransa na Abia wajen ziyarar jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a gidan yari.
Shugaban matatar man Dangote kuma hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote, ya ba da tabbacin cewa dogon layin neman man fetur ya zama tarihi a Najeriya.
Tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami, ya musanta zargin cewa yana da hannu cikin masu daukar nauyin ta'addanci. Ya ce akwai siyasa a cikin zargin.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yaba da sulhun da aka yi da 'yan bindiga. Ya ce sulhun ya jawo an samu zaman lafiya a yankunan da ke fama da matsala.
Shugaban jam'iyyar ZLP, Dan Nwanyanwu, ya ja kunnen tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan fitowa takara a zaben shekarar 2027. Ya tuna masa baya.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya shigar da kara kan sanata mai wakiltar Kogi ta Kudu a majalisar dattawa, Sanata Natasha Akpoti.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari