Manyan Labarai A Yau
Hukumar shari'a ta Najeriya (NJC) ta fara gudanar da bincike kan wasu manyan alkalai. Babbar alkalin alkalai ta damu matuka kan girman zarge-zargen da ake yi.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika sako ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, yayin buda baki da sauran gwamnonin Najeriya. Ya ce ya yi farin cikin ganinsa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi taron buda baki da gwamnonin Najeriya. Shugaba Tinubu ya dauko batun shirinsa na kawo karshen rashin tsaro.
Hadimin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya koka kan ci gaba da tsare shi da hukumar ICPC take yi. Ya bayyana cewa hukumar ta ki sauraron bukatar beli.
Majalisar dattawan Najeriya ta rasa wasu daga cikin mambobinta tun bayan kafuwarta a shekarar 2023. Wasu daga cikin sanatocin sun koma ga mahaliccinsu.
"Yan ta'addan Lakurawa sun kai harin kwanton bauna kan tawagar babban kwamandan rundunar Operation Fansan Yamma. Dakarun sojoji sun yi artabu da su.
'Yan ta'addan Boko Haram dauke da makamai sun kai wani harin ta'addanci a jihar Adamawa. 'Yan ta'addan sun farmaki wani sansanin sojoji tare da yin kisa.
Malamin addinin Musulunci a jihar Kaduna, Sheikh Halliru Maraya, ya yi wani zargi kan Malam Nasir El-Rufai. Ya nuna cewa bai yi Kiristoci adalci ba.
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya kai karar hukumar ICPC gaban kotu, yana kalubalantar samamen da ta kai gidansa a birnin Abuja.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari