Manyan Labarai A Yau
Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya bar PDP ya koma APC, inda ya shiga kara jerin gwamnonin da suka fice daga jam’iyyar tun bayan zaben 2023.
An bayyana Gwamna Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani na jam'iyyar Accord, hakan na zuwa ne awanni bayan ya yanki kati.
Tsohon mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, a yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan matakan da ya dauka saboda rashin tsaro.
An nada sababbin sarakuna kan karagar mulki a Arewacin Najeriya. Daga cikin sarakunan akwai wadana aka sababbin masarautu yayin da wasu kuma sun dade a tarihi.
Wata kotun jiha a Plateau ta yanke wa jami'in dan sanda, Ruya Auta hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan an kama shi da laifin kashe ɗalibin UNIJOS, Rinji Bala.
Julius Bokoru ya zargi EFCC da karya doka bayan ta zana “EFCC—Keep Off” a gidan tsohon minista Timipre Sylva, yana cewa an rufe gidan ba tare da wata sanarwa ba.
A kokarin dakile yaduwar juyin mulki, kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma watau ECOWAS ta kakaba dokar ta-baci a duka yankunan da ke karkashinta.
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da bukatar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar mata, inda yake neman tura dakarun sojoji zuwa Benin.
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya yi kira da babbar murya ga matasa. Atiki ya bukaci matasa su tashi tsaye ka da su zama 'yan kallo.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari