Manyan Labarai A Yau
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya tabbatar da tattaunawa da shugaban kasar Iran, Massoud Pezeshkian inda ya ce yana so a daina kai hari Gabas ta Tsakiya.
Runduar Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) ta kai hari kan wani sansanin sojojin Amurka da ke Bahrain. IRGC ta kai harin ne a matsayin ramuwar gayya.
Birtaniya ta sahalewa Amurka ta yi amfani da sansanoninta biyu domin kare kanta daga hare-haren kasar Iran, jiragen Amurka sun fara sauka a wuraren.
Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi a wasu sassa na birnin Legas. Tashin farashin man fetur din dai na da nasaba da yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.
Gwamnatin kasar Amurka ta amince da sayarwa Isra'ila makaman da za ta ci gaba da amfani da su wajen yakin da take yi. Gwamnatin ta tsallake majalisa.
Akwai alamun da ke nuna cewa wasu daga cikin ministocin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, za su yi murabus daga mukamansu. Ministocin za su sauka kan wasu dalilai.
Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya yi magana kan batun taimakon da Rasha ke ba Iran a yakin da ake yi. Ya bayyana cewa Amurka na sane da komai.
Wani malamin addini a kasar Ghana, Fasto Telvin Adjei Sowah, ya yi hasashe kan yakin Iran, Amurka da Israila. Ya ce ya hango abubuwan da za su faru a yakin.
Mayakan kungiyar Hezbollah sun yi arangama da dakarun sojojin kasar Isra'ila. Fadan da aka gwabza ya jawo an raunata wasu sojojin Isra'ila ciki har da dan Minista.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari