Manyan Labarai A Yau
Matatar Dangote ta sanar da rangwame a farashin kowace litar fetur, tare da rage litar dizal a Najeriya, wannan ne karo na farko bayan tashin danyen mai a duniya.
Shugaban Majalisar tarayyar Turai, Antonio Costa ya bayyana bisa abubuwan da ke faruwa a kasuwar duniya, Rasha ta fi amfana da yakin Iran, Amurka da Isra'ila.
Kotun daukaka kara ta zartar da hukunci a shari'ar da ake yi da gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, kan bukatar sake neman wa'adi na uku a kan mulki.
Farashin danyen mai ya sauka a kasuwannin duniya biyo bayan kalaman da shugaban kasar Amurka ya yi kan Iran. Iran ma ta mayar masa da martani mai zafi.
Jakadan Iran Najeriya, Gholamreza Mahdavi Raja, ya bayyana abin da Amurka da Isra'ila ke son cimmawa ta hanyar kai hare-hare a kasarsa. Ya ce akwa wata manufa.
Mayakan kungiyar Boko Haram sun kaddamar da hare-hare kan sansanonin sojojin Najeriya a jihar Borno, wadanda suka jawo asarar rayukan kwamandoji.
Wasu sanatoci na jam'iyyar Democrats a kasar Amurka sun bukaci a gudanar da bincike kan wani hari da ake zargin dakarun sojojin kasar sun kai a Iran.
Mayakan kungiyar Hezbollah da ke kasar Lebanon sun yi wa dakarun sojojin Isra'ila kwanton bauna yayin da ake ci gaba da fada. Sun lalata kayan aikinsu.
Shugaban Amurka, Donald J. Trump ya bayyana cewa kasarsa da hadin gwiwar Isra'ila sun yi nasarar lalata duk wani karfi na Iran, don haka an kusa dakatar da yaki.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari