Manyan Labarai A Yau
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, na neman hanyoyin da za su sanya Iran ta saduda kan mashigar ruwa ta Hormuz. Trump na duba yiwuwar yi wa Iran kwace.
Rundunar IRGC ta Jamhuriyar Musulunci ta kasar Iran ta kaddamar da sababbin hare-hare kan Isra'ila. Ta bayyana cewa za ta ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya.
Babban kwamanda a rundunar sojojin Iran ya bayyana tanadin da suka yi wa shugaban kasar Amurka, Donald Trump. Ya ce sun shirya masa abin ban mamaki.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kaddamar da sabon makami mai linzami a yakin da take yi da Isra'ila. Ta bayyana wuraren da ta farmaka a cikin kasar Isra'ila.
Rundunar IRGC ta kasar Iran ta yi ikirarin farmakar jirgin yakin Amurka. Mahukunta a Amurka sun tabbatar da cewa jirgin ya samu matsala a sararin samaniya.
Gwamnatin tarayya ta bullo da wani shiri da za a rika bai wa yan Najeriya damar samun rancen kudin sayen tikitin jirgin sama,daga bisani kuma su biya a hankali.
Hukumar Kula da Harkokin Sufurin Jiragen Kasa ta shirya zirga-zirga jirage ta musamman domin taimakawa jama'a a lokacin shagulgulan karamar Sallah.
Wasu daga cikin dakarun sojojin Isra'ila sun yi baya-baya da fagen daga inda suka ki zuwa wuraren aikinsu. Sojojin sun bayyana dalilinsu na yin hakan.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ayyana ranar Juma'a, 20 ga watan Maris, a matsayin ranar idin karamar Sallaha a Najeriya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari