Manyan Labarai A Yau
Tsohon firaministan Isra'ila, Ehud Barak, ya caccaki Benjamin Netanyahu kan yakin da ake yi da Iran. Ehud Barak ya zargi Netanyahu da yin karya kan yakin.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta shirya gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai a gaban kotu kan wasu tuhume-tuhume.
Dakarun sojojin Najeriya sun kai wani artabu a sansanin tantirin jagoran 'yan bindiga, Bello Turji. Sojojin sun samu gagarumar nasara a farmakin da suka kai.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya fara tattauna da kasar Iran don samun mafita a yakin da ake yi. Iran ta yi martani kan wannan ikirarin.
Hukumar kula da sufurin ruwa ta kasa (NIWA) ta yi martani kan rahotannin da ke cewa wasu 'yan bindiga sun nutse a cikin kogi a Sokoto bayan jirginsu ya yi hatsari.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a wata coci da ke jihar Kwara. 'Yan bindigan sun sace masu ibada da dama yayin harin da suka kai.
Ministan kudin Amurka, Scott Bessent, ya yi tsokaci kan batun ci gaba da daukar nauyin yaki da Iran ta fuskar kudade. Ya yi watsi da batun kara haraji.
Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta yi martani kan barazanar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi wa Iran.
Wani rahoto da hukumar NISO ta fitar ya nuna cewa fatan samun wadatacciyar wutar lantarki a Najeriya na kara samun koma baya cikin yan shekarun da suka shige.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari