Manyan Labarai A Yau
Hasashe ya nuna 'yan Najeriya miliyan 141 za su rayu cikin talauci a 2026; fadar shugaban ƙasa ta yi watsi da waɗannan alƙaluma, tare da fadin matakan da aka dauka.
Kwanaki kaɗan bayan sauya shekar Peter Obi zuwa ADC, Datti Baba-Ahmed ya ayyana shiga takarar shugaban ƙasar Najeriya a 2027 ƙarƙashin jam’iyyar LP,
Bayan MRS, an samu karin gidajen mai da suka hada kai da matatar Dangote kuma kungiyar IPMAN na ganin hakan zai zama alheri a farashin fetur a Najeriya.
Yara 469 ne suka mutu a Kano sakamakon rashin abinci mai gina jiki a 2025; UNICEF ta bayyana cewa kashi 51.9% na yara a jihar suna fama da matsalar tsumburewar jiki.
An gano wani babban makami mai linzami a yankin Mashegu na jihar Neja wanda ake zargin na Amurka ne; jami’an tsaro sun kwashe makamin zuwa Minna a yau don bincike.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina. Tsagerun sun yi awon gaba da mutane masu yawa zuwa daji.
An fito da wani tsohon bidiyo na gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, yana nuna tsantsar biyayyarsa ga Rabiu Musa Kwankwaso. Ya ce ba zai masa butulci ba.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada manufofi, Daniel Bwala, ya yihasashen abubuwan da za su faru da Peter Obi a jam'iyyar ADC a zaben 2027
Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya yaba da salon mulkin jam'iyyar APC. Ya bayyana cewa ita ce jam'iyyar da ta dace da mulkin Najeriya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari