Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta karfafa gwiwar tawagar 'yan wasan Super Eagles kan wasan da su yi da Morocco.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bukaci jama'a ka da su tsaya suna fada da miyagun masu aikata laifuffuka. Ta ce kare rai ya fi tsayawa yin fada.
Gasar AFCON 2025 na ci gaba da gudana a kasar Morocco. Akwai wasu zaratan sababbin matasan 'yan wasa da suka dauki hankula. Akor Adams na Najeriya na cikinsu.
Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi martani kan tallafin kayan aikn sojoji da Amurka ta ba Najeriya. Ya ce ya kamata sauran kasashe su taimaka.
Kasar Amurka ta shigo da kayan aiki na sojoji ga dakarun Najeriya. An shigo da kayan aikin ne kwanaki kadan bayan kawo hari kan 'yan tadda a Sokoto.
Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya bayyana cewa kudaden da ake ba gwamnoni duk wata sun karu. Ya bukaci su yi wa jama'a abin da ya dace.
Gwamnatin Saudiyya ta ja kunnen Najeriya kan illar watsi da marayu da yara marasa galisu, ta ce hakan zai iya zama babbar barazana ga tsaron kasa.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a jihar Benue. 'Yan bindiga sun hallaka wasu matafiya da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba bayan sun farmake su.
Dan gwagwarmaya kuma lauya mai rajin kare hakkin dan adam, Deji Adeyanju, ya ragargaji 'yan adawa kan maganganun da suke yi dangane da shari'ar Abubakar Malami.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari