Manyan Labarai A Yau
Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yi tsokaci kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita. Ya ce kasashen waje ba za su iya magance matsalar ba.
Ministan tsaro, Christopher Musa ya bayyana cewa akwai abubuwan da ke rura wutar matsalar rashin tsaro. Ya bayyana cewa dole a tsare iyakokin Najeriya.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya ce dojar harajin sa aka yi za ta kaow ci gaba mai dorewa idan mutane suka bai wa gwamnatin Najeriya hadin kai 100%.
Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma jigo a jam'iyyar ADC, Dele Momodu, ya bayyana cewa akwai yadda 'yan adawa za su iya kifar da Bola Tinubu a 2027.
Tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina kuma jigo a jam'iyyar ADC ya yi zargin cewa wata karamar hukuma ta ware kason 'yan bindiga a kasafin kudinta.
Gwamnatin tarayya ta yaba da jarumtar da 'yan wasan Super Eagles suka nuna a wasan da suka yi da Morocco. Ta ce 'yan Najeriya na alfahari da su duk da rashin nasara.
Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya gwangwaje sarakunan gargajiya da kyautar manyan motoci na alfarma domin tallafa masu wajen gudanarda ayyukansu.
Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya yi garambawul a gwamnatinsa. Gwamnan ya sauya wa wasu daga cikin kwamishinoninsa ma'aikatun da za su jagoranta.
Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya bayyana tsare-tsaren da suka yi na birne mataimakinsa, Mr Lawrence Ewhrudjakpo, wanda ya rasu a watan Disamba, 2025.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari