Manyan Labarai A Yau
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari ta'addanci a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto. Sun kashe mutane tare da raunata bayin Allah.
Tsohon ministan sufuri kuma tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa 'yan adawa su kuka da kansu kan rashin nasarar da suke yi a zabe.
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya dauki matakin kokar daya daga cikin hadimansa. Korar da aka yi masa na da nasaba da zanga-zangar da aka yi a jihar.
Babban jami'in kula da walwala na tafiyar Kwankwasiyya, Saddam Sani Umar, ya bayyana cewa sauya shekar Gwamna Abba Kabir zuwa APC ba za ta jawo asara a Kwankwaso ba.
Wata fitacciyar jarumar fim a Najeriya, Doris Ogala ta bayyana cewa da alamu ba za ta yi tsawon rai ba aaboda abin da Fasto Okafor ya mata na yaudara a soyayya.
Babbar kotun jihar Rivers mai zama a Fatakwal ta umarci babban alkalin jihar da kada ya karbi takarda ko bin umarnin Majalisa game da tsige Gwamna Siminalayi Fubara.
Fitaccen malamin addinin kirista a Najeriya, Bishop Isaac Idahosa ya yaba waGwamna Umaru Bago saboda matakan da yake dauka na kawar damatsalar taaro a Neja.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya tashi daga Abuja zuwa Guinea-Conakry domin wakiltar Bola Ahmed Tinubu a bikin rantsar da Mamadi Doumbouya.
Gwamnatin jihar Sokoto ta fito ta yi martani kan rahotannin da aka yada cewa 'yan bindiga sun farmaki mutane da matsugunansu. Ta ce ba kamshin gaskiya a batun.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari