Maiduguri
A cikin wannan labarin za ku ji cewa hukumar bayar da agajin gaggawa ta SEMA ta bayyana ceto mutane 3,682 da ambaliyar ruwa ta tare a jihar Borno.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ruwan da ke shiga madatsar Alau ne ya fi karfinta, wanda ya sa ta fara neman hanyar fita zuwa cikin gari ta sama.
Wadanda suka tsira daga ambaliyar ruwa a Maiduguri sun ba da labarin abin da ya faru yayin da 'yan agaji ke kara kaimin ceto wadanda suka makale.
A labarin nan, za ku ji dan majalisar Borno mai wakiltar yankunan Biu/Bayo/Shani/Kwaya/Kusar, Mukhtar Betara ya mika jaje ga wadanda iftila'in ambaliya ya fada wa.
Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa a kalla mutane miliyan 2 sun shiga matsala bayan ambaliya. Zulum ya ce akwai karancin abinci da yunwa a Maiduguri.
Bayan duba irin barnar da ambaliyar ruwa ta yi a Maiduguri, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya ba gwamnatin Borno tallafin N50m da jiragen ruwa.
Gwamnatin tarayya, ta bakin hukumar raya shiyyar Arewa maso Gabas ta bayyana cewa rashin kargon gini da cushewar ruwa a madatsar Alau ya jawo ambaliya a Maiduguri.
Gwamnatin Najeriya ta kashe N26m domin aikin gyaran madatsar Alau a ranar 29 ga watan Yulin 2024, kusan wata daya kafin ambaliyar ruwa ta mamaye Maiduguri.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta ce zuwa yanzun ta gano gawarwakin mutum 30 waɗanda suka rusu a ambaliyar ruwan da ta kusa shafe Maiduguri.
Maiduguri
Samu kari