Lafiya Uwar Jiki
Kwararrun lafiya na kasar Habasha sun tabbatar da cewa, Mista Odemu ya yi ido biyu da ajali bayan da cutar kajamau wadda ta shahara da karya duk wata garkuwar jiki ta yi masa rikon kazar kuku da a dole sai da ta kai shi ga faduwa.
Tsawon shekaru aru-aru 'baure wani nau'in dangin kayan marmari ne da ya shahara a duniya ta fuskar dandano da kuma amfani ga lafiya. Wani bincike da jaridar Guardian ta wallafa ya bayyana muhimmancin baure wajen magance cututtuka.
Kankana ta kasance daya daga cikin 'ya'yan itatuwa mafi shahara a doron kasa kuma mutane da dama su kan yi santi kwarai yayin kwankwadar ruwanta musamman wadanda kwayoyin halittun su masu bambance dandano ke aiki kwarai.
Idan aka ce Hepatitis, toh ana nufin ciwon Hanta kenan a Hausance. Hepatitis kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka hada da; Hepatitis A, Hepatitis B, Hepatitis C, Hepatitis D, Hepatitis E.
A yau ne ranar ciwon hanta ta duniya wato World Hepatitis Day. Allurar riga kafin ciwon hanta wasu allurori ne guda uku zuwa hudu da ake yi na tsawon watanni 6. Ba'a kamuwa da ciwon hanta matukar an yiwa mutum alluran riga kafi.
A cewar jaridar kasar Ingila (Daily Mail UK), matar ta sanar da mahaifyarta cewa ta na jin kasala kuma ga shi ba ta iya cin abinci kafin daga bisani ta fadi a sume, lamarin da yasa aka garzaya da ita zuwa asibiti. A cikin dakin ak
Alamomin cutar hanta sun rabu kashi daban-daban daga kanana zuwa manya. Su kan bayyana a jikin dan Adam bayan wata daya zuwa watanni hudu da kamuwa da cutar. A wani sa'ilin su kan bayyana bayan mako biyu da kamuwa.
Babu shakka masana sun yi itifakin cewa rashin gamsuwa a wurin saduwar iyali a tsakanin ma'aurata na daya daga cikin manyan dalilai dake haddasa matsaloli da a wani sa'ilin take janyo mutuwar aure.
Masana sun bukaci jama’a da su dunga yawan cin gwaza domin cewa yana dauke da sinadarai masu matukar amfani a jikin dan adam. Bincike ya kuma nuna cewa ganyen gwaza na dauke da sinadarin kawar da cututtuka da suka hada da makanta.
Lafiya Uwar Jiki
Samu kari