Wani sabon maganin zazzabin cizon sauro dake maida jinin mutum guba ga sauro

Wani sabon maganin zazzabin cizon sauro dake maida jinin mutum guba ga sauro

- Wani sabon salon yaki da zazzabin cizon sauro ya fito. Zazzabin cizon sauro ita ce cutar da ta fi kisa a yankin Afirika. A yayin da masana suka yi bincike sun gano maganin dake sa jinin dan'adam ya zamo guba ga sauro tare da halaka duk kwaron da ya zuki jinin mutum.

Wani sabon maganin zazzabin cizon sauro wanda ke kashe sauro idan yasha jinin mutum
Wani sabon maganin zazzabin cizon sauro wanda ke kashe sauro idan yasha jinin mutum

Wani sabon salon yaki da zazzabin cizon sauro ya fito. Zazzabin cizon sauro ita ce cutar da ta fi kisa a yankin Afirika. A yayin da masana suka yi bincike sun gano maganin dake sa jinin dan'adam ya zamo guba ga sauro tare da halaka duk kwaron da ya zuki jinin mutum.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar PDP ta nuna goyon bayanta akan sake salon zabe

Binciken ya nuna cewa saurayen dake dauke da cutar suna mutuwa ne bayan sun sha jinin dan'adam din da ya sha maganin mai suna IVERMECTIN. Ivermectin magani ne dake daya daga cikin ajin magunguna mai suna antihelmintics. Aikin sa shine shanye jinin jikin kwari da kuma kashe su. Idan akayi ma mutum allura da kwatankwacin yawan da ya dace, jinin bawai kawai yana korar sauro bane ba, yana maida jinin guba ga sauron na tsawon wata daya a yanda binciken ya nuna.

Wata kungiyar bincike data samu jagorancin turawa ta raba ma' aikata 139 daga kasar Kenya zuwa kashi uku. Binciken ya nuna cewa Idan akayi ma da Dan'adam allura da 300mcg/kg shine mafi daidai a jikin dan'adam domin kuwa yana kaiwa kwanaki 28 a jikin Dan'adam. Kashi 97 na sauro kan mutu ne cikin sati biyu bayan sun sha jinin dan'adam mai dauke da maganin.

Wannan sabon binciken zai zamo abin alfahari ga yan Najeriya da kuma Afirika wadanda suke da kaso mafi yawa a duniya na cutar. Kamar yanda kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta fada a shekara ta 2016, cutar ta kashe mutum dubu 429 kuma ta kama mutum miliyan 212 a Afirika. Ta tabbatar da cewa yara masu shekaru kasa da biyar sunfi kamuwa da cutar. Kashi 70 daga cikin su kan rasa rayukansu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng