Jerin Jihohi 16 da suka sha fama da cutar Sankarau a Najeriya
Tarihi ya bayyana cewa a shekarar 1996 kadai, kimanin rayuka 11, 717 ne suka salwanta a sanadiyar cutar Sankarau da ta kunno kai a wancan lokaci, inda wasu rayuka 1, 525 suka salwanta a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2009.
Cutar Sankarau ta ci gaba da ta'azzara cikin al'ummar kasar nan musamman na yankin Arewacin ta, inda a ranar Juma'a wanda ta daidai da 31 ga watan Maris na shekarar da ta gabata, kimanin mutane 328 suka ce ga garin ku nan.
A yau shekara guda kenan da wallafar jaridar Vanguard ta yi a ranar 4 ga watan Afrilun shekarar da ta gabata, inda ta jeranto jihohi 16 da cutar Sankarau da daidaita a wancan lokaci.
KARANTA KUMA: Yadda cutar hawan jini da ciwon hanta ke yiwa 'yan Najeriya kisan mummuke
Cikin kananan hukumomi 90 na kasar nan, jaridar Legit.ng ta kawo muku sunayen jihohin kamar haka; Zamfara, Katsina, Sakkwato, Birnin tarayya, Kebbi, Jigawa, Gombe, Taraba, Yobe da kuma Nasarawa.
Sauran jihohin da cutar Sankarau ta kwashi rabon ta sun hadar da; Kano, Osun, Neja, Cross River, Legas da kuma jihar Filato.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng