Riga kafi ya fi magani: Da ka ji alamun nan guda 14, ka je ka fara maganin cutar Siga

Riga kafi ya fi magani: Da ka ji alamun nan guda 14, ka je ka fara maganin cutar Siga

Lafiya uwar jiki, kamar yadda dan Hausa ke fadi, a wannan zamani da muka tsinci kanmu a ciki da jama’a basu cika damuwa da abubuwan da suke ci ba, sakamakon yawaita ababen ci, musamman kayan kwalam da makulashe, hakan ta kai ga jama’a na kamuwa da cututtuka da dama.

Guda daga cikin cututtukan da jama’a ka iya kamuwa da su sun hada da cutar Siga, wanda ke nufin halin da sigar dake jikin mutum ta yi sama fiye da yadda jikin ke bukatarta, don haka ake shawartar jama’a da a dinga ziyarar Asibiti domin samun kwararrun Likitoci su yi gwaje gwaje don tabbatar da matsayin sigar jikin mutum.

KU KARANTA: Tsohon mataimakin shugaban kasa, tsohon gwamna kuma Sanata ya shiga zawarcin mukamin gwamna a Filato

Legit.ng ta kawo muku manyan alamu guda 14 dake nuni da kodai mutum ya kamu da cutar siga ko kuma yana gab da kamuwa da ita, Alah ya kyauta.

1- Yawan jikin kishi a kulli yaumin

2- Maimaituwar wata cuta ko ciwo a jiki

3- Rashin samun haihuwa

4- Kan jiki, wato daukan dogon lokaci kafin ciwo ko yanka ya warke a jikin mutum

5- Busashshen baki

6- Yawan fitsari a cikin dare

7- Yawan Kasala

8- Matsananciyar yunwa

9- Busashshen fata mai yawan kaikayi

10- Ciwo a jijiyoyi

11- Kiba da tara kiste a mara

12- Ganin dishi dishi

13- Rashin samun nutsuwa

14- Lalacewar ciki tare da ciki ya dinga yawan kugi

Sai dai ganin wadannan alamu baya nufin babu sauran damar rayuwa bane, ko kuma ace mutuwar ta zo ba, a’a, sai dai ana bukatar mutumin dake ganin alamun nan ya dakatar da cin nau’o’in abinci irin su farar shinkafa, Burodi, masara, cincin, dankali da sauransu.

Hakazalika ya zama wajibi irin wannan mutumi ya dukufa wajen cin nau’o’in abinci kamar su Karas, naman Talatalo, abarba, ayaba, lemu, taliya, wake, kashu, tumatir, da sauransu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng