Ababe 3 dake haddasa cutar Sankarau a Najeriya

Ababe 3 dake haddasa cutar Sankarau a Najeriya

A yayin da cutar Sankarau ta sake kunno kai a Najeriya kamar yadda ta afku a wasu lokuta na baya inda take addabar wasu jihohi, Legit.ng cikin kalace-kalacen da ta saba ta kawo muku jerin wasu ababe ukku dake haddasa wannan cuta a kasar nan.

Allurar riga kafi ta cutar Sankarau
Allurar riga kafi ta cutar Sankarau

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta na shirin tsare-tsaren dakatar da kashe-kashe a Birnin Gwari - Dambazzau

Cutar Sankarau tana da nasaba ne da wasu kwayoyin cuta da a turance ake ce da su Bacteria da kuma Virus, wanda suke shiga cikin kwakwalwa da kuma kashin baya na dan Adam su yi lahani.

Wani bincike da kwararren masanin kiwon lafiya ya gudanar, Dakta Ahmad Gana ya bayyana wasu ababe dake haddasa cutar Sankarau kamar haka:

1. Kwanciya ko zama inda mutane suke taruwa da yawa.

2. Shakar numfashi mutane a wurin da babu wadatacciyar iska.

3. Rashin yin alluran riga-kafi na cutar sankarau.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel