Wata Mata ta hau dokin zuciya, ta yi sibarnabayyen wata jaririya yar wata 8
Wata Kotun Karmo ta umarci a garkame mata wata mata mai suna Theresa Obonna a Kurkuku sakamakon kamata da tayi da laifin satar jaririya mai watanni takwas kacal a Duniya.
Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito Alkalin Kotun, Abubakar Sadiq ya daure Obonna duk da cewa ta musanta zargin, daga nan ya dage sauraron karar zuwa ranar 3 ga watan Mayu.
KU KARANTA: Sun gagari kundila: Wasu manyan matsaloli guda 3 da suka gagari shugaba Buhari
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dansanda mai kara Zannah Dalhatu ya bayyana ma Kotu cewa wani mutumi mazunin jihar Akwa Ibom, Godstime David ne ya kai kara zuwa ofishin Yansanda dake Life Camp a Abuja a ranar 2 ga watan Maris.
Dalhatu yace David ta zargi saurayinta be ta dirka mata ciki a watan Janairu na shekarar 2017, inda ya bukaci ta zubar da cikin, amma taki, inda ta tsere zuwa Abuja, har ta haife jaririyar, bayan nan ne sai wanda ake kara ya dauke jaririyar.KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Sai dai Dansandan yace amma sakamamon zuzzurfan bincike sun samu nasarar gano inda aka boye jaririyar, sa’annan ya kara da cewa laifin ya saba da sashi na 288 na kundin hukunta manyan laifuka.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng