Wani matashi ya yanke jiki ya fadi ya mutu sakamakon shan kwayoyin Taramol
- Wani matashi mai shekaru 25 ya mutu a jihar Deltata ta sanadiyar shan kwayoyin tramol
- Hukumar harkan kiwon lafiya ta garagdi matasa akan illar shan kwayoyin Tramol
Legit.ng ta samu rahoton cewa wani matashi mai shekaru 25 ya yanke jiki ya mutu bayan ya sha wasu kwayayoyi da ake zargin kwayoyin Taramol ne.
Al’amarin ya faru a yankin Abaraka, dake karamar hukumar, kudncin jihar Delta, a karshen makon da ta gabata.
Bincike ya nuna matashin wanda sanannen dan kabukabun keke Napep ne a yankin ya dade yana amfani da kwayoyin taramol.
KU KARANTA : Mamora yaki karban sabuwar mukamin da Buhari ya bashi
Rahotannin sun nuna cewa, matashin ya yanke jiki ya fadi ne a gaban wani baban shagu dake kan baban titin Abraka, kafin mutane suka garzaya dashi asibiti inda ya cika anan.
Hukumar harkan kiwon lafiya na Najeriya ta yi gargadi akan illar shan kwayoyi tramol ga matasa musamman ga ‘da namiji, saboda tramol yana hana namiji haihuwa kuma yana fitar da mutum daga cikin hayacin shi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng