Nigerian news All categories All tags
Kiwon lafiya: Magani 16 da shan ruwa da safe kafin cin komai ke yi

Kiwon lafiya: Magani 16 da shan ruwa da safe kafin cin komai ke yi

Kamar yadda masanna suka tabbatar, ruwa shine abinda jikin dan adam yafi bukata fiye ma da abinci domin dan adam na iya rayuwa ba tare da cin abinci ba na tsawon watanni amma kwanaki 3-4 kawai mutum ke iya rayuwa ba tare da shan ruwa.

Ruwa ne ke taimakawa jikin dan adam kawar da guba, daidaita sinadarai na jini da kuma taimakawa wajen numfashi, fitar ta bayan gida, da isar jini zuwa dukkan sassan jiki.

Kamar yadda muka samo daga binciken da cibiyar lafiya ta gudanar, jikin galibin maza yana bukatar kofi 12 ko lita 3 na ruwa a kullum, su kuma mata jikinsu na bukatar a kalla kofi 8 ko kuma lita 2.

Binciken har ila yau ya bayyana cewa lokacin da ruwa shan ruwa yafi amfani a jikin dan adam shine lokacin da mutum ya farka da safe kafin ya yi kalaci. Kuma ana bukata ne mutum ya sha dai-dai yadda jikinsa ke bukata domin rashin ruwa a jiki na iya haifar da matsaloli da dama.

Kiwon lafiya: Magani 11 da shan ruwa da safe kafin cin komai ke yi

Kiwon lafiya: Magani 11 da shan ruwa da safe kafin cin komai ke yi

Ba kowa bane ya sani amma bincike ya nuna cewa shan ruwa idan an farka da safe na iya samar da sauki ko magance wadannan cututukan.

1) Ciwon al'ada na mata

2) Ciwon kunne

3) Basir

5) Amai da Gudawa

6) Kumburin ciki

7) Rashin zuwa bayan gida

8) Hawan jini

9) Ciwon koda

10) Ciwon sankarau

11) Ciwon farfadiya

12) Ciwon gabobin jiki

13) Ciwon kai

14) Saukin Ciwon suga

16) Ciwon mahaifa

Yadda ake amfani da shan ruwa don magance wasu daga cututukan da aka ambata:

Ana bukatar mutum ya sha kofi 4 na ruwa bayan ya farka daga barci, sai kuma ya jinkira cin abinci har sai bayan minti 45.

Haka zalika, bayan mutum ya karya, sai ya jinkirta shan ruwa kuma sai bayan sa'o'i 2 kafin nan sai mutum ya cigaba da shan ruwa kadan-kadan.

Ga masu fama da rashin bayan gida da gyambon ciki , ana bukatar suyi kwanaki 10 suna shan ruwan, masu ciwon suga da masu hawan jini kuma kwanaki 30, sai masu tarin TB kuma kwanaki 90.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel