An kama dan leken asirin kungiyar Boko Haram a Kano
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce ta kama wani mutum dake aikin leken asiri ga kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram a garin Wudil, ranar 24 ga watan Maris.
Mutumin, Sanusi Bello, an kama shi da wayoyin hannu da kuma katinan shaidar aiki masu yawa, ciki har da na hukumar 'yan sandan Najeriya da kuma na wani makwabcinsa dan kungiyar bijilanti da kudi, N37,857.
Kazalika a jihar Neja, hukumar ta ce, ta kama wani mutum dake samar da makamai ga masu sace mutane. An kama shi ne a hanyar sa ta kai makamai ga 'yan ta'adda a jihar Edo.
Ko a ranar 23 ga watan Maris, saida jami'an hukumar suka kama wani mutum, Mathew Ekam; mai shekaru 39, wanda ke da hannu cikin satar Obiajunu Onyema.
A wani labarin na Legit.ng mai alaka da wannan, kun ji cewar, kungiyar 'yan bijilanti a jihar Katsina ta yiwa mutane 1,200 rijista domin taimakawa jami'an tsaro a jihar wajen hana aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram.
DUBA WANNAN: Madallah: Shugaban kungiyar Basalube ta masu garkuwa da mutane a jihar kogi ya shiga hannu
Shugaban kungiyar bijilanti a jihar, Alhaji Abba Mainayara, ya sanar da hakan a ganawar sa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN).
Tun shekarar 2009, kungiyar Boko Haram take aiyukan ta'addanci da ya yi sanadiyar dubban mutane tare da raba wasu da dama da muhallinsu, a arewacin Najeriya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng