Yadda cutar hawan jini da ciwon hanta ke yiwa 'yan Najeriya kisan mummuke

Yadda cutar hawan jini da ciwon hanta ke yiwa 'yan Najeriya kisan mummuke

Da sanadin kamfanin dillancin labarai wata kungiya mai zaman kanta ta Moole Charity Foundation ta bayyana cewa, manyan matsaloli dake janyo salwantar rayuka a Najeriya sune cutar hawan jini da kuma ciwon hanta watau Hepatitis.

Dakta Linda Odoh, shugaba ta wannan kungiya ita ta bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai dangane da shirin wayar da kai da suka gudanar a babban birnin kasar nan na Abuja.

Odoh take cewa, zuwa duban asibitoci akan kari zai taimaka kwarai da aniyya wajen dakile barazana da hadurra da wannan cututtuka ke tafe da su.

Ministan Lafiya; Farfesa Isaac Adewole
Ministan Lafiya; Farfesa Isaac Adewole

Take cewa, sun gudanar da wannan shiri ne domin aiwatar da gwaje-gwaje kyauta ga al'umma akan cututtukan hawan jini, ciwon suga, ciwon hanta, zazzabin cizon sauro da kuma cutar kanjamau mai karya garkuwar jiki.

Dakta Odoh ta ci gaba da cewa, bincike ya tabbatar da cewa musabbabin mace-mace dake ta afkuwa a halin yanzu ba wani ba wani abu bane face cututtukan masu yiwa dan kisan mummuke ba tare an farga ba.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan lamari ya sanya cibiyar ta gudanar da gwaje-gwajen ta kan al'umma tare da wayar musu da kai da kuma fadakarwa.

KARANTA KUMA: Jerin sunayen manyan Kabilu da jihohin su a Najeriya

Dakta Odoh ta shawarci al'umma akan su yawaita motsa jiki, cin kayan itatuwa da ganye akan kari tare da gargadin su akan kauracewa barasa da kuma ta'ammali da sigari domin hakan zai taimaka matuka wajen inganta lafiyar su.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta kudiri aniyya ta kawo karshen ta'addanci da ya yi kamari a jihar Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng