Labarin Sojojin Najeriya
Gwamnatin Borno ta yi gyara kan adadin tubabbun yan Boko Haram da su ka tsere daga wurin da ake ba basu horo. Gwamnatin ta ce mutum shida ne su ka gudu.
Wasu yan bindiga da aka yi wa luguden wuta a Zamfara sun fara neman mafaka a jihar Kano. An gano cewa yan bindiga sun mallaki gidaje a unguwannin Kano.
Rundunar sojan sama ta Najeriya (NAF) ta fitar da ka’ida ga wadanda suka kammala karatu a manyan makarantu kuma suke da sha'awar shiga aikin sojan a bangaren DSSC.
Sojojin Najeriya sun harbe jagoran yan ta'adda da ake kira da Mai Hijabi a jihar Jigawa. Haka zalika sojojin Najeriya sun kashe miyagu da yan bindiga a jihohi.
Sojojin Najeriya sun kama manyan yan bindiga uku da suka fitini al'umma a jihohin Taraba da Filato tsawon shekaru. An kama wanda yake musu safarar makamai.
Sojojin Najeriya sun taru sun lakadawa dan sanda duka kuma ya mutu har lahira. Sojojin sun yi rundugu ga dan sandan yayin da wani soja ya kira su ta wayar tarho.
Yan ta'addar Boko Haram da suka tuba ana ba su horo domin taimakon sojoji da bayanai sun tsere da makamai, suna barazanar kai hare hare kan al'umma.
Ministan tsaro, Bello Matawalle ya ce za su canza salon yaki da yan bindiga wajen hana yan ta'adda yawo a jihohin Arewa. Matawalle zai ziyarci jihohin Arewa uku.
Wasu tsagerun 'yan bindiga sun kai hari a jihar Imo. Jami'an tsaro na sojoji sun fito sun fafata da su lamarin da ya jawo asarar rayuka tare da raunata wasu mutane.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari