Labarin Sojojin Najeriya
Dakarun sojojin saman Najeriya sun kai hari kan 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno. Sojojin sun hallaka 'yan ta'adda masu yawa tare da lalata makamai masu yawa.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi magana kan kuskuren da jami'an tsaro suka yi wajen jefa bama-bamai kan fararen hula a kauyukan Sokoto.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan 'yan ta'adda masu kai hare-hare a sassa daban-daban na kasar nan. Sun hallaka miyagu tare da cafke masu aikata laifuka.
Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta yi magana kan jirage marasa da matuka da 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP suka fara amfani da su wajen kai hari a fagen daga.
ECOWAS ta karyata cewa Najeriya na goyon bayan ta’addanci a Nijar. Kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ba Najeriya gaskiya a sabaninta da makwabciyarta.
Darektan harkokin yada labarai na hedikwatar tsaro, Manjo Janar Edward Buba ya ce ba bam ya kashe mutane ba. Janar Buba ya ce an yi nasara ba a yi barna sosai ba.
Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar cafke wani da ake zargin dan ta'addan Boko Haram ne a jihar Taraba. Dakarun sojojin sun kuma cafke wani jami'in tsaro.
Wata mata ta bayyana yadda iyayenta suka kone kurmus tare da 'yan uwanta bayan harin da jirgin Soji ya kai a Gidan Sama da Runtuwa, Silame, Jihar Sokoto.
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato ya bayyana cewa gwamnatinsa ta tuntubi hukumomin soji domin bincike kan kuskuren kashe fararen hula a kauyuka.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari