Labarin Sojojin Najeriya
Hatsabibin shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, ya umarci mayakansa da su yi wa dakarun sojoji kwanton bauna. Umarnin na Bello Turji na zuwa ne bayan an kashe dansa.
Bello Turji ya yi barazana ga mazauna kauyukan kusa da Shinkafi, yana cewa zai kai hare-hare ga masu zuwa kasuwa. Jami'an tsaro na ƙara zage dantse wajen kamo shi.
Jami'an tsaro da suka hada da 'yan sanda, sojoji, DSS da sauransu sun samu nasarar dakile wani harin 'yan bindiga a jihar Katsina. Sun kwato shanun da aka sace.
Yayin da gwamnatin Zamfara ta bayyana cewa ta na kokari wajen tallafawa wadanda harin Zamfara ya shafa, yayin mutanen Kaduna da Sakkwato ke jiran dauki.
Rundunar sojojin Najeriya ta kai hari har sansanin 'yan bindiga da su ka addabi jihohin Kebbi da Sakkwato, inda aka kashe miyagun yayin da wasu su ka gudu.
Sojoji biyar sun mutu yayin samame kan ƴan ta'adda a Sakkwato; an kashe ƴan ta'adda shida, an kwace bindigu da harsasai yayin da aka nemi nemi goyon bayan jama'a.
Hedkwatar sojojin Najeriya watau DHQ ta bayyan cewa wasu mayaka daga ƙasashen ketare sun shigo Najeriya, suna da hannu a hare haren da aka kai kwanan nan.
Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro a sassa daban-daban na kasar nan, sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda kusan 200 a fafatawar da suka yi.
'Yan ta'adda sun kai wa sojoji da fararen hula hari a Borno, inda aka rasa mutane da dama yayin aikin kwaso gawarwakin manoma da aka kashe a yankin Dumba.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari