Labarin Sojojin Najeriya
Tinubu ya ƙaddamar da ginin sansanin sojoji a Abuja, ya yi alkawarin tallafi da inganta jin daɗin sojojin Najeriya yayin da ƙarancin gidaje ya zama kalubale.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci sojoji da su shiga cikin dazuzzuka domin fatattakar 'yan bindigan da suke boye a ciki.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bukaci gwamnatin Katsina ta goyi bayan shirin da ta bullo da shi na yin sulhu da 'yan bindiga domin kawo karshen rashin tsaro.
Dakarun sojojin sama sun yi ruwan wuta kan 'yan bindiga a jihar Neja. Sojojin sun hallaka 'yan bindiga masu tarin yawa a hare-haren da suka kai a sansaninsu.
Rundunar tsaron Najeriya ta sanar da kashe mataimakin Bello Turji mai suna Aminu Kanawa yayin farmaki. An kashe wasu tarin mayakan dan ta'addar a Sokoto da Zamfara.
Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai, sun samu nasarar dakile wani hari da 'yan ta'addan ISWAP suka yi yunkurin kai wa a jihar Yobe.
Gwamnatin jihar Sokoto karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu, ta bukaci mutanen Gabashin jihar da su sanya ido kan 'yan ta'addan da ke tserewa sojoji.
Yan ta'addan Boko Haram dauke da makamai sun kai hari a jihar Borno. Dakarun sojoji sun fafata da 'yan ta'addan inda suka fatattake su bayan an yi gumurzu
Mutanen karamar hukumar Batsari a jihar Katsina, sun nuna takaicinsu kan sulhun da gwamnati ta yi da 'yan bindiga. Sun bayyana cewa hakan bai da amfani.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari