Labaran Duniya
Yayin da aka doshi kwana na shida ana rigima tsakanin Iran da Isra'ila, Majalisar Dinkin Duniya ta nemi a gaggauta kawo karshen rikicin da tattaunawar diflomasiyya.
Iran ta harba makamai masu linzami sama da 100 kan Isra'ila. An rahoto cewa makaman da Iran ke harbawa na isa Isra'ila cikin mintuna 12 saboda tsananin gudu.
Wani masanin sufurin jiragen sama, Captain Steve, ya na ganin cewa kuskuren matukin jirgi na bude fuka-fukai maimakon dage tayar jirgi ne ya jawo hatsarin Air India.
Rahotanni daga Isra'ila sun nuna cewa yahudawa ƴan ƙasar Isra'ila sun fara guduwa daga gidajensu suna zama a tashoshin jiragen kasa saboda hare-haren Iran.
Jagoran juyin juya hali na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya nuna cewa kasarsa ba za ta nuna tausayi ba a yakin da take yi da haramtacciyar gwamnatin Isra'ila.
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Cif Femi Fani-Kayode ya nuna damuwarsa kan kalaman barazana da Donal Trump ya yi gameda jagoran addinin Iran.
Bayan nazarin abin da ke faruwa a rikicin Iran da Isra'ila, akwai bukatar mu kalli tasirin rikicin kasashen ga tattalin arzikin duniya, musamman farashin mai.
Gidan talabijin na Iran ya sanar da kai hare-hare karo na 10 a jerin farmakin ramuwar gayya da kasar ke kai wa kan Isra'ila bayan ɓarkewar rikici tsakaninsu.
Rasha ta kai hari mai tsanani kan Kyiv, inda ta kashe mutane 15. Shugaba Zelenskyy ya kira harin da mafi muni yayin da ya nemi kasashen duniya su ce wani abu.
Labaran Duniya
Samu kari