Labaran Duniya
Rundunar 'yan sandan Washington DC da ke Amurka, ta tabbatar da cewa an harbi sojojin kasa biyu har sun aamu raunuka a kuaa da fadar White House.
Rahotanni daga kasar Guinea-Bissau sun tabbatar da cewa dakarun sojoji sun kifar da gwamnati, sun sanar da dakatar da shirin zzabe tare da rufe iyakokin kasar.
Fitaccen jarumin Bollywood Dharmendra Deol ya rasu yana da shekaru 89 a Mumbai. Ya fito a fina-finai 300, ya bar babban tarihi a masana’antar fina finan Indiya.
Matsalar fasaha ta Cloudflare ta haddasa durkushewar shafukan intanet da dama, ciki har da X, ChatGPT da su Letterboxd yayin da kamfanin ke ci gaba da bincike.
Jam'iyyar APC reshen Amurka ta shiryya tura tawaga zuwa Majalisar dokokin USA domin gabatar da hakikanin ci gaba da aka samu a yaki da ta'addanci a Najeriya.
Majalisar dinkin duniya ta amince da kudirin kafa rundunar tsaron duniya a Gaza. Kudirin zai taimaka wajen kafa kasar Falasdinawa a shekaru masu zuwa.
’Yan sanda a New Orleans sun kama wani matashi dan Najeriya, Chukwuebuka Eweni, bisa zargin kashe mahaifinsa da raunata ’yan uwansa mata biyu a cikin gida.
Yan majalisar dokonin jamhuriyar Benin sun tsawaita wa'adin shugaban kasa zuwa shekaru bakwai, sun ce babu wanda zai wuce wa'adi biyu a kan gadon mulki.
Mutane shida sun mutu a wajen cunkoson daukar aikin sojoji a Accra, Ghana. Gwamnati ta dakatar da shirin kuma Shugaba Mahama ya ziyarci wadanda suka ji rauni.
Labaran Duniya
Samu kari