Labaran Duniya
Wani yaro dan shekara 13 ya ceci mahaifiyarsa da kannensa daga teku bayan ya yi iyo na tsawon awa hudu a Australia, Jami’an ceto sun yaba da jarumtakarsa.
Kasar Amurka ta gargadi yan kasarta kan ziyartar Nijar a 2026, saboda tabarbarewar tsaro da ayyukan ta’addanci, tare da sabbin sharuddan tafiye-tafiye.
WHO ta gano bullar cutar Nipah a Indiya; cuta ce mai saurin kisa, lalata kwakwalwa, kuma ba ta da magani. Ga abin da ya kamata ku sani game da hadarin ta a 2026.
Agogon da ke hasashen tashin duniya ya kara cillawa gaba da dakika 85 a karon farko bayan shiga 2026. An bayyana cewa barazana na karuwa a fadin duniya a halin yanzu
Hukumomin kasar Colombia sun tabbatar da cewa duk mutanen da ke cikin jirgin Satena da ya bata jiya Laraba, sun mutu a hatsarin da ya rutsa da su.
Ana sa ran fara azumin Ramadan 2026 a ranar 19 ga Fabrairu; za a azumci sa'o'i 12 zuwa 13 cikin sanyi, wanda ke nuna sauki ga Musulmi a wannan shekara.
An kai wa Ilhan Omar hari da allura mai dauke da sinadarin ruwa a Minneapolis; an kama maharin yayin da take sukar hukumar ICE a ranar 27 ga Janairu, 2026.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa yana tura manyan jiragen yaki Gabas ta Tsakiya kusa da Iran a halin yanzu domin jiran ko ta kwana.
Hukumar kare hakkin dan dama ta majalisar dinkin duniya, OHCHR ta bukaci kasashe da su daina yankewa mutane hukuncin kisa bayan fitar da rahotonta na 2025.
Labaran Duniya
Samu kari