Labaran Duniya
Birtaniya ta sahalewa Amurka ta yi amfani da sansanoninta biyu domin kare kanta daga hare-haren kasar Iran, jiragen Amurka sun fara sauka a wuraren.
Kasar Qatar ta bayyana cewa ha za ta yarda da irin hare-haren da Iran ke kai wa cikin yankinta ba, ta tura wasiku biyu ga Majalisar dinkin duniya.
Shugaban Majalisar dinkin Duniya, Antonio Guterres ya bayyana cewa idan ba a yi gaggawar shawo kan rikicin Gabas ta Tsakiya ba, zai iya fin karfin kowa.
Gwamnatin kasar Amurka ta amince da sayarwa Isra'ila makaman da za ta ci gaba da amfani da su wajen yakin da take yi. Gwamnatin ta tsallake majalisa.
Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya yi magana kan batun taimakon da Rasha ke ba Iran a yakin da ake yi. Ya bayyana cewa Amurka na sane da komai.
Wani malamin addini a kasar Ghana, Fasto Telvin Adjei Sowah, ya yi hasashe kan yakin Iran, Amurka da Israila. Ya ce ya hango abubuwan da za su faru a yakin.
Fadar White House ta tabbatar da cewa shugaban kasa, Donald Trump ya shirya halartar taron karbar dakarun sojojin Amurka shida da Iran ya yi ajalinsu a Kuwait.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an tattauna ta waya tsakanin Shugaba Vladimir Putin da takwaransa na Iran kan yakin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya.
Firaminiatan Qatar, Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani, da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi sun yi magana ta waya jan hare-haren kasar.
Labaran Duniya
Samu kari