Kwankwasiyya
Dan Majalisa mai wakiltar Ƙiru da Bebeji, Abdulmumini Ƙofa ya bayyana cewa jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso ne kaɗai zai iya yanke shawara kan sauya sheƙa zuwa APC.
Karamin ministan gidaje da raya birane a gwamnatin Bola Tinubu daga Kano, Yusuf Ata ya ce APC na da shirin lashe gwamnan jihar a zaɓen shekarar 2027.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa Sai'du Yahya a matsayin sabon shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.
Jam'iyyar NNPP ta ce ba za ta hukunta dan majalisar NNPP kuma aboki tafiyar Rabiu Kwankwaso ba saboda ganawa da Bola Tinubu a fadar shugaban kasa.
Fasto Francis Udo ya bayyana cewa Godswill Akpabio zai kasance mataimakin shugaban kasa a tikitin Rabi'u Musa Kwankwaso bayan Bola Tinubu ya kammala.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya karɓi bakuncin ɗam Majalisar Wakilai daga Kano, Hon. Abdulmumini Kofa a Aso Rock, ya yi maganar Sanata Kwankwaso.
Fadar shugaban kasa ta ce alakar shugaba Bola Tinubu da Rabiu Kwankwaso ba sabuwa ba ce, kuma babu laifi idan sun hada hanya a siyasar Najeriya a gaba.
Jam'iyyar NNPP ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya daina tankawa Rabiu Musa Kwankwaso. Ta ce so yake ya yi a rika kula shi don ya yi suna.
Jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya ta shawarci matasan yankin Arewa da su yi taka tsan-tsan da madugun Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwankwasiyya
Samu kari